26 Afirilu 2020 - 06:15
Ghana: Shugaba Akufo Ya Taya Musulmi Murnar Shiga Watan Ramadan

Shugaban na kasar Ghana Nana Akufo-Addo wanda ya fitar da bayanin taya musulmi shigowar watan azumi, ya bayyana cewa;

(ABNA24.com) “Mu na yi wa musulmi kyakkyawan fata acikin wannan watan na azumi, kamar kuma yadda mu ke rokon Allah madaukakin sarki da ya albarkace mu baki daya, da kuma kasarsmu, ya kuma mayar da ita mai karfi.

Shugaban kasar na Ghana ya bayyana azumin watan Ramadana da cewa; lokacin ne na yawaita ibada da sadaukar da kai da nuna kauna da kuma kyautata ayyuka.

Har ila yau shugaban na kasar Ghana ya yi fatan ganin al’ummar musulmi sun ci gaba da aiki da darussan da su ka koya a cikin watan azumin, hatta bayan Ramadan.

Al’ummar musulmi a kasar Ghana sun kai kaso 17% a kasar da yawan mutanenta ya karaci miliyan 30.



/129